Iran Ta Nuna Damuwarta Dangane Da Goyon Baya Ido Rufe Da MDD da WHO Suke Nunawa Rigakafin Amurka

2021-01-12 09:02:14
Iran Ta Nuna Damuwarta Dangane Da Goyon Baya Ido Rufe Da MDD da WHO Suke Nunawa Rigakafin Amurka

Wani babban jami’in kiwon lafiya na ƙasar Iran ya nuna tsananin damuwarsa dangane da irin nuna wariya da kuma goyon baya ido rufe da cibiyoyin ƙasa da ƙasa irin su Majalisar Dinkin Duniya (MDD) da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suke nunawa magunguna da rigakafin da kamfanonin Amurka suke samarwa da kuma ci gaba da matsin lamba ga sauran ƙasashe na su yi amfani da waɗannan magunguna waɗanda ba a riga da an tantance amfani da kuma cutarwarsu ba.

Shugaban cibiyoyin kimiyyar likitanci na ƙasar Iran, Sayyid Alireza Marandi ne ya bayyana hakan cikin wata wasiƙa da ya aike wa babban sakataren MDD, Antonio Guterres, inda yayi kakkausar suka ga shirun da cibiyoyin ƙasa da ƙasa irin su MDD da kuma WHO ɗin suka yi dangane da takunkumin zaluncin da Amurka ta sanya wa ɓangaren likitanci na ƙasar Iran wanda hakan wani Karen tsaye ne ga haƙƙin ƙasar.

Dr. Marandi ya ƙara da cewa: Cutar COVID-19 ta shafi dukkanin ƙasashen duniya kamar yadda kuma ta fi cutar da wasu ƙasashen daga ciki kuwa har da Iran, amma duk da hakan cibiyoyin ƙasa da ƙasa da kuma ƙungiyoyin da suke ikirarin kare haƙƙoƙin bil’adama sun yi gum da bakunansu kan takunkumin zaluncin da aka sanya wa Iran.

A wani ɓangare na wasiƙar tasa, jami’in kiwon lafiyan na Iran ya nuna damuwarsa kan yadda cibiyoyin ƙasa da ƙasa ɗin suke nuna goyon bayansu ido rufe musamman ga rigakafin cutar nan ta COVID-19 da kamfanonin Amurka suka samar da kuma ci gaba da matsin lamba wa sauran ƙasashen duniya wajen su yi amfani da su.

Al’ummomin duniya da dama dai suna ci gaba da sanya shakku cikin rigakafin da kamfanonin Amurka irin su Pfizer suka samar na cutar ta COVID-19 saboda rashin tabbas da suke da shi.

A Iran ma Jagoran juyin juya halin Musulunci na ƙasar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya hana amfani da waɗannan rigakafin na Amurka.


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!