Jiragen Yakin Faransa Suna Shawagi A Kan Birnin Bangui Na Afirka Ta Tsakiya

2021-01-10 14:09:20
Jiragen Yakin Faransa Suna Shawagi A Kan Birnin Bangui Na Afirka Ta Tsakiya

Jiragen yakin kasar Faransa sun fara shawagi kan babban birnin kasar Afirka ta tsakiya Bangui bayan da ‘yan tawaye suka kai hare–hare kan garuruwa biyu kusa da babban birnin kasar.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa Faransa tana son hana ‘yan tawaye mamayan babban birnin kasar ne, bayan rikicin siyasar da ya kunno kai bayan zabe shugaban kasa a karshen shekarar da ta gabata.

Dakarun tabbatar da zaman lafiya na MDD, MINUSCA a takaice, suna sintiri a kan titunan babban birnin kasar ne tun kafin a gudanar da zaben a cikin watan Disamban da ya gabata.

A jiya Asabar ce gamayyar ‘yan tawaye magoya bayan tsohon shugaban kasar Francois Bozize suka kai hari kan garuruwan Bouar mai tazarar kilomita 440 daga babban birnin kasar da kuma Grimari mai tazarar kilomita 300 shi ma daga Bangui babban birnin kasar. Sannan sun yi barazanar kwace birnin.

Hukumar zaben kasar ta bayyana cewa shugaban mai ci ne Faustin-Archange Touadera ne ya lashe zaben da kasha fiye da 50%. Wata kotu ta hana Buzize tsayawa takarar shugabancin kasar.


19

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!