​Najeriya: Buhari Ya Ce Zai Yi Yaki Da Tsadar Abinci A Cikin Shekara Ta 2021

2020-12-30 20:39:36
​Najeriya: Buhari Ya Ce Zai Yi Yaki Da Tsadar Abinci A Cikin Shekara Ta 2021

Shugaban Najeriya Mohammed Buhari ya yi alkawarin cewa, gwamnatinsa za ta yaki matsalar hauhawar farashin kayayyakin abinci a sabuwar shekara mai kamawa.

Shugaban ya yi alkawarin ne a yayin taronsa karo na biyar da Kwamitin Tattalin Arziki na fadar shugaban kasa a birnin Abuja.

Shugaban ya kuma umarci babban bankin kasar CBN da ka da ya bai wa ‘yan kasuwa kudi domin shigo da abinci daga ketare, yana mai cewa, a yanzu akwai jihohi bakwai a Najeriya da ke samar da shinkafar da ta wadaci kasar, kuma dole mu ci abin da muke nomawa a cewarsa.

Tun bayan rufe iyakokin da gwamnatin Najeriya ta yi, aka samu karancin shinkafar da ake shigowa da ita a cikin kasar, musamman ma dai wadda ake shigo da ita ta kaniyakoki na kasa.

Wasu daga cikin manoman shinkafa a kasar sun yaba da daukar wannan mataki, domin kuwa a cewarsu hakan ya basu damar yin noma da kuma samun riba mai yawa.

Wannan na zuwa ne a lokacin da wasu yankunan da ake fama da matsalolin tsaro suke kokawa da samun babban cikas wajen gudanar da ayyukan noma, saboda barazanar da suke fuskanta daga ‘yan ta’adda, wanda hakan yasa a wasu yankunan aikin noma ya tsaya baki daya.

Hauhawar farashin kayayyakin abinci da ma kayan masarufi baki daya yana daya daga cikin abin da yake ci ma al’umma tuwo a Najeriya, ta yadda farashin yake ninkawa a kasuwanni da sauran wuraren hada-hadar kasuwanci, wanda hakan yakan shafi rayuwar jama’a ta yau da kullum.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!