​Yemen: Akalla Mutane 22 Sun Rasa Rayukansu Bayan Tashin Wasu Bama-Bama A Filin Jirgin Aden

2020-12-30 19:27:28
​Yemen: Akalla Mutane 22 Sun Rasa Rayukansu Bayan Tashin Wasu Bama-Bama A Filin Jirgin Aden

Rahotanni daga kasar Yemen na cewa, a yau wasu bama-bamai sun tashi a lokacin da ministocin gwamnatin Mansur Hadi ke isowa filin sauka da tashin jiragen sama da ke birnin Aden a kudancin kasar.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, an ji wasu abubuwa masu matsananciyar kara sun fashe a cikin filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Aden a kudancin kasar Yemen.

Rahoton ya ce lamarin ya auku ne a daidai lokacin da tawagar ministocin gwamnatin Mansur Hadi da ke da matsugunni a birnin Riyad na kasar Saudiyya, take isowa filin jirgin daga Riyad.

Lamarin dai ya faru ne a daidai lokacin da takun saka yake ta kara kamari tsakanin bangarorin da suke mara baya ga kawancen da ke kaddamar da yaki kan kasar ta Yemen, inda bangarorin da ke samun goyon bayan Saudiyya da suka hada da bangaren Hadi Mansur, suke zaman doya da manja da bangarorin da ke samun goyon bayan hadaddiyar daular larabawa.

Sai faruwar lamarin ke da wuya, sai gwamnatin Hadi ta zargi kungiyar Ansarullah (Alhuthi) da cewa ita ce ta kai harin, yayin da ita kuma kungiyar ta bayyana cewa ba ta hannu a cikin lamarin, ta da bayyana cewa hakan wata manuniya ce kan babban sabanin da ke tsakanin bangarorin da suke yaki da al’ummar kasar, inda suka fara kashe junansu ba tare da rahma ba.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!