Adadin Wadanda Su Ka Kamu Da Cutar Covid-19 A Nahiyar Afirka Sun Haura Miliyan 2

2020-12-29 15:01:50
 Adadin Wadanda Su Ka Kamu Da Cutar Covid-19 A Nahiyar Afirka Sun Haura Miliyan 2

A wani rahoto da jaridar Ghana Times ta buga ta ambaci cewa a jiya Litinin an tabbatar da cewa adadin mutanen da su ka kamu da cutar ta covid-19 a fadin nahiyar Afirka sun kai miliyan 2,508,815, yayin da wadanda su ka rasa rayukansu kuwa sanadiyyar cutar sun kai 59, 099.

Wannan kididdigar dai ta fito ne daga cibiyar hana yaduwar cutuka ta nahiyar Afirka da aka fi sani da ( Africa CDC)

Dangane da kasashen da cutar ta fi yi wa illa kuwa, rahoton ya ambaci Afirka ta kudu, Moroko, Masar da Habasha.

Wadanda su ka kamu a cutar a Afirka ta Kudu su kai 921,922, sai kuma wasu mutanen 24,691 da su ka rasa rayukansu.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!