​Wata Tagawar Masar Ta Isa Birnin Tripoli Na Kasar Libya A Yau

2020-12-27 19:54:47
​Wata Tagawar Masar Ta Isa Birnin Tripoli Na Kasar Libya A Yau

Wata tawagar jami’an gwamnatin kasar Masar ta isa birnin Tripoli na kasar Libya domin ganawa da jami’an gwamnatin Tripoli.

A bisa rahoton kamfanin dillancin labaran Fars News da kuma rahotanni da kafofin yada labarai na kasashen Masar da Libya suka bayar, tawagar ta kasar Masar ta isa Tripoli a yau bayan kwashe shekaru 7 wata tawagar Masar ba ta saka kafarta a birnin ba.

Ministan harkokin cikin gida na gwamnatin Tripoli Fathi Bashaga ne ya tarbi wannan tawaga, kuma ya tattauna da su a kan muhimman lamurra da suka shafi halin da ake ciki kasar.

Wasu rahotanni sun ce, tawagar ta Masar za ta bukaci gwamnatin Tripoli da ta takatar da karbar makamai daga gwamnatin Turkiya, kuam ta fitar da mayakan da Turkiya ta shigo da su cikin kasar Libya.

Wanann dai na zuwa ne a daidai lokacin ministan tsaron kasar at Turkiya ya kai ziyara a kasar Libya tare da wasu manyan hafsoshin sojin kasar, domin jaddada ci gaba da kasancewa a Libya.

Gwamnatin masar dai na daga cikin gwamnatocin kasashen larabawa da suke taimaka ma Khalifa Haftar da ke iko da gabashin kasar ta Libya, ayyin da Turkiya ke taimaka ma gwamnatin Tripoli.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!