A kalla Bakin Haure Yan Afirka 20 Ne Suka Mutu Bayan Da Kwale-Kwalensu Ya Nutse A Teku

2020-12-24 22:15:13
A kalla Bakin Haure Yan Afirka 20 Ne Suka Mutu Bayan Da Kwale-Kwalensu Ya Nutse  A Teku

Rahotanni sun bayyana cewa kimanin bakin haure guda 20 ne da suka fito daga kasashen Afrika suka rasa rayukansu bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya nutse a lokacin da suke kokarin ketare tekun Midetereniya zuwa tsibirin Lampedusa na kasar Italiya, sai dai an yi nasarar ceto mutane biyar daga cikinsu.

Kakakin ma’aikatar tsaro na kasar Tunisiya Mohammad Zakri ya fadi cewa kwale-kwalen ya nutse a cikin ruwan ne bayan da ya yi tafiyar mil 6 da gabar teku, inda nan ne wurin da masu kokarin yin hijira zuwa kasashen turai ta barauniyar hanya suke tashi saboda gujewa talauci da ke addabar wasu kasahen Afrika da na gabas ta tsakiya.

Idan ana iya tunawa ko a tsakiyar watan Disamba ma sai da masu gadin teku na kasar Tunusiya suka ceto yan gudun hijira 93 da suka fito daga kasashen Afrika daban – daban cikin har da yan asalin kasar Tunisiya guda 3.

Maakatar harkokin cikin gidan kasar Tunusiya ta fadi cewa tsakanin farkon shekara zuwa watan Satumba kimanin mutane 8581 ne aka cafke dake kokarin tsallakawa zuwa kasahen turai ta gabar tekun kasar Tunisiya.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!