Search
Close this search box.

Rasha: Murkushe zanga-zangar goyon bayan Falasdinu A Amurka ya saba wa dokokinta na ‘yanci

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta sanar da cewa, mummunan martanin da mahukuntan Amurka suka mayar a kan zanga-zangar goyon bayan Falasdinu a kasar, ya

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta sanar da cewa, mummunan martanin da mahukuntan Amurka suka mayar a kan zanga-zangar goyon bayan Falasdinu a kasar, ya saba wa dokokin Amurka kan ‘yancin fadin albarkacin baki.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta fada a taron manema labarai cewa: “A bayyane yake cewa hukumomin Amurka sun dogara ne kan tarwatsa masu zanga-zangar da karfi, da kuma kwashe tantunansu da jami’an ‘yan sanda na musamman suka yi da karfi.”

Ta kara da cewa: “Amurka ta yi mu’ama da dalibai ‘yan kasarta ta hanyar da ta sabawa dukkan dokokinta da suka shafi ‘yanci, bayyana ra’ayi da kuma ‘yancin gudanar da taro, Har ila yau, kuma Amurka ba ta yi aiki da nauyin da ya rataya a kanta ba bisa dokokin kasa da kasa.

Sannan kuma ta nanata cewa abin da ke faruwa wani misali ne na bin salon siyasar harshen damo da rashin daidaito a cikin siyasar Amurka.

Zakharova ta ci gaba da cewa: “Sun fi son tallafa wa masu zanga-zanga a ko’ina cikin duniya, amma idan ana batun masu zanga-zangar a cikin Amurka, a lokacin na’urarsu ta azabtarwa take aiki yadda ya kamata.”

Zanga-zangar dalibai domin goyon bayan Falastinu, da ke kira a kawo karshen kisan gillar da Isra’ila take yia  Gaza na ci gaba da kara bazuwa a Jami’o’in Amurka.

‘Yan sandan Amurka sun mamaye harabar jami’o’i da dama, tare da tarwatsa zaman dirshan na dalibai masu nuna goyon bayansu ga Gaza, a daidai lokacin da rahotanni ke cewa an kama dalibai da dama a fadin kasar.

Zanga-zangar ta hada da Washington, D.C., da wasu jihohi, yayin da kungiyoyin kare hakkin bil’adama suka yi tir da cin zarafin dalibai masu zanga-zangar.

Kamfanin dillancin labaran AP ya bayar da rahoton cewa, jami’an tsaron Amurka sun kama akalla mutane 2,000 a zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu a jami’o’i a Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments