Search
Close this search box.

MDD Ta Yi Gargadi Game Da Hadarin Da Ke Tattare Da Kai Harin Isra’ila A Rafah

Kakakin ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi game da hadarin da ke tattare da hare-haren Isra’ila a kan

Kakakin ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi game da hadarin da ke tattare da hare-haren Isra’ila a kan birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza.

Gwamnatin yahudawan sahyuniya da ke ci gaba da kai hare-hare a yankuna daban-daban na zirin Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023, na shirin kai hari kan birnin Rafah, birnin da ke da dimbin ‘yan gudun hijira Falasdinawa.

Kamfanin dillancin labaran Saba na kasar Yaman ya bayar da rahoton cewa, kakakin ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a wani taron manema labarai a birnin Geneva a jiya Juma’a, ya yi gargadi cewa, duk wani hari da gwamnatin sahyoniyawa za ta kai kan birnin Rafah na iya haifar da kashe fararen hula masu yawa, tare da jefa rayuwar dubban daruruwan mutane cikin hadari.

Tashar talabijin ta Aljazeera ta kasar Qatar ta bayar da rahoton cewa, mayakan gwamnatin sahyoniyawa sun yi ruwan bama-bamai a unguwar “Al-Zahor” da ke arewacin birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza, inda a sakamakon haka wasu fararen hula Palasdinawa shida suka yi shahada.

A wani harin da harin da sojojin yahudawan suka kaddamar ta sama a sansanin “Al Brij” da ke tsakiyar zirin Gaza, fararen hula sun jikkata.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya laifukan da yahudawan sahyuniya suka aikata a yankin Zirin Gaza sun kara yawan talauci zuwa sama da kashi 90% a tsakanin al’ummar Gaza, kuma za a dauki shekaru 80 ana aiki kafin a iya sake gina yankin zirin Gaza.

Ya zuwa yanzu Isra’ila ta kashe Falasdinawa akalla 34,622. Fiye da Falasdinawa 77,867 kuma sun sami raunuka a cikin watanni 7 da take kaddamar da hare-haren kisan kare dangi kan al’ummar yankin zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments