Sojojin Yamen sun sanar da fara aiwatar da wani sabon mataki na hare-haren ramuwar gayya a kan masu taimaka ma Isra’ila a kisan kare dangin da take kan al’ummar yankin zirin Gaza.
A cikin wata sanarwa a ranar Jumma’a, Yahya Saree, mai magana da yawun sojojin Yemen, ya ba da sanarwar fara aiwatar da kashi na hudu na sabon farmaki domin taimakon al’ummar Gaza.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, matakin ya zo ne a daidai lokacin da ake sa ran Isra’ila take shirin mamaye kudancin birnin Rafah, inda kusan rabin al’ummar Gaza masu yawan mutane 2.4 suka nemi mafaka daga hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a sauran wurare da ke Gaza.
A cewar sanarwar, sojojin Yemen, a karkashin sabon matakin, za su kai hari kan dukkan jiragen ruwa da ke zuwa tashoshin jiragen ruwa na Isra’ila ta hanyar Tekun Bahar Rum.
Saree ya yi gargadin cewa sojojin Yaman za su kuma “kakaba takunkumi mai tsauri” kan dukkan jiragen ruwa na kamfanonin da ke da hannu wajen samarwa Isra’ila da kayayyaki, ba tare da la’akari da kasashensu ba, da kuma “hana duk jiragen ruwa na wadannan kamfanoni wucewa ta hanyar ruwan tekun Red Sea, matukar dai Isra’ila ta kaddamar da harin da take shirin kaiwa yankin Rafah a Gaza.