Isra’ila Ta Sake Fadawa A Wani Sabon Rikicin Siyasa

2020-12-23 15:02:17
Isra’ila Ta Sake Fadawa A Wani Sabon Rikicin Siyasa

Isra’ila ta sake fadawa wani sabon rikicin siyasa, bayan rusa majalisar dokoki ta Knesset da yammacin jiya Talata.

Hakan ya sanya za’a sake kiran ‘yan Isra’ilar domin kada kuri’a a watan Maris na shekara mai shirin kamawa, wanda kuma shi ne zabe karo na hudu da za’ayi a kasa da shekaru biyu.

Masana dai na ganin ba za’a iya magance rikicin siyasar na Isra’ila ba muddin Benjamin Netanyahu yaka kan madafun iko.

Duk abunda ke faruwa na rusa majalisa da kiran zabe wani yunkuri ne Netanyahu na ya ci gaba da jan ragamar gwamnati, har zuwa lokacin da zai gurfana gaban kotu kan zargin da ake masa na cin hanci da rashawa.

A watan Janairu na shekara mai zuwa ne ta 2021 aka tsara Netanyahun zai gurfana gaban kotu.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!