Tawagogin Manazarta Daga MDD Za Su Shiga Yankin Tigray Na Habasha

2020-12-22 09:44:12
Tawagogin Manazarta Daga MDD Za Su Shiga Yankin Tigray Na Habasha

Tawagogi biyu na MDD za su ziyarci yankin Tigray na Habasha mai fama da rikici, domin tantance bukatun jin kai da ake da su a yankin.

Stephane Dujarric, kakakin Sakatare Janar na MDD, ya ce tawaga daya za ta ziyarci yankin Shire yayin da dayar kuma za ta tafi yankin Mekelle.

Manufar ziyarar da ake sa ran za ta shafe mako guda ita ce, tantance bukatun jin kai da ake da su a yankunan

A kwanan baya dai Majalisar Dinkin Duniya, da kuma gwamnatin Habasha, sun cimma wata sabuwar yarjejeniya kan batun yankin Tigray, domin shirya yadda za’a isar da kayan tallafi ga jama’ar yankin, kamar yadda babban sakataren MDD, Antonio Guteress ya sanar.

A bisa matsayar da bangarorin suka cimma, za’a samu damar shiga lungu da tsako na yankin domin gudanar da ayyukan jin kai ba tare da nuna bangaranci ba a cewar MDD.

Mutane kimanin 50,000 ne suka kauracewa rikici a yankin inda suke kwarara zuwa cikin makobciyar kasar Sudan.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!