Jagora Ya Jinjina Wa Ma’akatan Jinya A Kan Sadaukarwar da Suke yi Domin Ceton Al'umma

Jagoran juyin juya
halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya yi jinjina ta musamman ga ma'aikatan jinya sakamakon
sadaukarwar da suke yi domin ceton rayuwar jama’a, tare da bayyana abin da suke
yi da cewa jihadi ne.
Jagoran ya bayyana
hakan ne a cikin wani jawabi da ya gabatar a yau, domin tunawa da ranar ma’aikata
masu jinya, wadda ake ba ta muhimmanci matuka a kasar Iran.
Ya ce ko shakka
babu ma’ikatan jinya suna da matsayi na musamman a cikin kowace al’umma ta
duniya, amma a wannan karo hakikanin matsayinsu na masu sadaukarwa domin ceton
rayuwar al’umma ya kara bayyana a wannan lokaci da ake fama da annobar corona.
Haka nan kuma ya
bayyana cewa, baya ga aiki na kula da jikin marassa lafiya da yi magani, suna
da wani aiki maimuhimmanci wanda shi ne karfafa maras lafiya tare da sanya shi
nishadi, domin rage masa damuwar da take da shi, wanda kuma wannan abu ne da
addinin muslucni ya yi umarni da shi.
Dangane da hakkokin
masu aikin jinya kuwa, jagoran ya bayyana cewa abu ne da ya rataya a kan jami’an
gwamnatin kasa, domin kuwa shi mai aikin jinya shi ne yake tare da maras lafiya
fiye da likita, saboda haka yana bukatar a dauke masa abubuwa da dama ta fuskar
rayuwarsa domin ya mayar da hankali ga aikin kula maras lafiya.
Haka nan kuma ya
bayar da misali kan yadda masu kula da maras lafiya akowane a asibiti suka fi zama wadanda cuta
tafi saurin kamawa, musamman a wannan zamani da ake fama da corona, inda masu
aikin jinyar marassa lafiya da dama suka kamu, wasu ma suka rasa rayuwarsu a
wanann aiki.
Daga karshe jagoran
ya yi fatan alhairi ga dukkanin al’umma musamman masu sadaukarwa domin sauran
al’umma su ci gaba da kasancewa a raye a cikin koshin lafiya, wanda kuma ma’aikatan
jinya da likitoci da sauran bangarori na kiwon lafiya suna gaba a wannan
bangare.
015