Amurka Ta Fara Janye Sojojinta Daga Kasar Somaliya

2020-12-19 20:18:39
Amurka Ta Fara Janye Sojojinta Daga Kasar Somaliya

Kafafen watsa labarun Amurka sun sanar da cewa sojojin kasar sun fara janyewa daga kasar Somaliya a bisa umarnin shugaban kasar Donald Trump.

Sanawar ta ci gaba da cewa tun a ranar 1 ga watan Satumba ne sojojin na kasar ta Somaliya.

Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta shaida wa kafafen watsa labarun kasar ta Amurka cewa; jiragen ruwa na yaki na Amurka da suka hada; USS Hershel,Woody Williams da ya kasance a gabatar ruwan Somaliya sun janye zuwa wani wuri a gabashin nahiyar ta Afirka.

Da akwai sojojin Amurka 700 girke a kasar ta Somaliya da suke bayar da horo ga sojojin gwmanatin kasar wacce take fada da kungiyar ‘al-shabab’ mai alaka da Alka’ida.

Sai dai sanarwar da Amurka ta ce sojojin kasar za su ci gaba da zama a wannan yankin domin gudanar da ayyukansu na fada da ta’addanci.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!