Gwamnatin Namibia Ta Fara Shirye-shiryen Karbar Riga-kafin Cutar Covi-19

2020-12-12 09:24:16
Gwamnatin Namibia Ta  Fara Shirye-shiryen  Karbar Riga-kafin Cutar Covi-19

Kasar Namibia ta kafa kwamitin kwararru domin yin shirye-shiryen yadda za a karbi riga-kafin cutar corona a fadin kasar.

Ministan kiwon lafiyar na kasar ta Namibia da ke kudancin Afirka,ya sanar da cewa an bai wa kwararru umarnin tantance wuraren da za aadana riga-kafin da kuma yadda za a rarraba shi a fadin kasar.

Mafi yawancin kamfanonin da suka samar da rika-kafin sun sanar da cewa da akwai bukatar wuraren masu matukar sanyi da za a adana maganin da kuma rarraba shi.

A bisa tsarin da gwammatin kasar ta fito da shi, tana son a matakin farko ta yi wa kaso 20% na al’ummar kasar allurar riga-kafin curar da ta zama annoba a duniya.

Ma’aikatan lafiya da masu yawan shekaru ne ake son fara yi wa allurar riga-kafin.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!