Majalisar Dokoki A Nigeria Ta Dakatar Da Gayyatar Da Ta yi Wa Shugabn Kasa Na Ya Bayyana A Gabanta

2020-12-10 22:46:09
Majalisar Dokoki A Nigeria Ta Dakatar Da Gayyatar Da Ta yi Wa Shugabn Kasa  Na Ya Bayyana A Gabanta

Da dukkan Alamu dai gayyatar da majalisar dokoki ta yi wa shugaban Nigeria Mohammadu Buhari na ya bayyana a gabanta na neman ya sha ruwa , bayan da aka ji shiru daga bangaren yan majalisar game da wannan gayyata.

Duk da tabbacin da kakakin majalisar wakilai ta kasa Gbajabiamila ya bayar na cewa shugaban Buhari ya amince ya bayyana a gaban majalisar a tsakanin 10-15 ga watan Disamba domin amsa wasu tambayoyi kan tabarbarewar tsaro.

Wannan yana zuwa ne bayan da ministan shari’a na kasar Abubakar malami ya bayyana cewa majalisar kasar ba ta da hurumin gayyatar shugaban kasar ya bayyana a gabanta don yin bayani game da matsalar tsaro da ya yi wa kasar katutu, musamman bayan kisan gillan da aka yi wa wasu Manoma 43 a garin Zamarbari na jihar Borno.

A nasa bangaren matakimakin shugaban masu rinjaye a majalisar Honorabul Toby Okechukwu ya bayayna cewa gayyatar da majalisar ta yi wa shugaban kasar a bisa doka take, kana ya zargi minsitan shari’ar da kokarin kare matsayin jami’iyar APC mai mulkin na kin amincewa shugaban ya bayyana a gaban majalisa domin amsa wasu tambayoyi kan tabarbarewar tsaro.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!