Amurka Ta Sanya Najeriya, A Jerin Kasashen Da Babu Yancin Gudanar Da Addini

2020-12-08 10:32:42
Amurka Ta Sanya Najeriya, A Jerin Kasashen Da Babu Yancin Gudanar Da Addini

Amurka ta sanya Najeriya, a cikin jerin kasashen data ce babu walwala ko ‘yancin gudanar da addini.

Dama dai a bara Amurka ta ce tana sanya ido sosai kan Najeriyar, akan abunda ya shafi yancin gudanar da addini.

Sakataren harkokin wajen Amurkar Mike Pompeo, ya bayyana a shafinsa na twitter cewa, Amurka tana sanya ido sosai akan abunda ya shafi yancin gudanar da addini, a don haka ne take sanya ido sosai da kuma daukar mataki idan har an takura wa wannan yancin.

Saidai M. Pompeo, bai bayyana takamaimai abunda Amurkar ke zargin Najeriyar da shi ba kan toye hakkin gudanar da addini.

Saidai a wani rahotonta data wallafa a baya cikin watan Yuni, kan yancin gudanar da addini a duniya, gwamnatin Amurka, ta nuna damuwa kan yadda mahukuntan na Najeriya ke amfani da karfin tsiya wajen murkushe ayyukan mabiya mazahabar shi’a, wanda y akai har ga haramta kungiyarsu, wanda bangarori daban daban na Najeriyar, suka danganta da babbar barazana ga yancin gudanar da addini a kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika.

Sauran kasashen da Amurkar ta nuna damuwa akan yancin gudanar da addinin a rahotonta na 2019, sun hada da Saudiyya, Myanmmar, China, Koriya ta Arewa, Eritrea, Da Iran, da Pakistan da Tadjikistan da kuma Turkménistan.

Saidai mafi akasarin wadannan kasashen na musatan rahoton na Amurka.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!