Rasha: Ba Za Mu Amince Da Rubuta Wata Sabuwar Yarjejeniya Kan Shirin Nukiliyar Iran Ba

Gwamnatin kasar Rasha ta sanar da
cewa, ba za ta amince da batun rubuta wata sabuwar yarjejeniya ka shirin Iran
na nukiliya ba.
Jakadan kasar Rasha a ofishin
majalisar dinkin duniya a birnin Vienna na kasar Austria Mikhail Ulyanov ne ya
sanar da hakan, inda ya ce abin da ke da muhimmanci shi ne dukkanin bangarorin
da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar da aka cimmawa a kan shirin na Iran, su
yi aiki da ita.
Ya ce tun bayan da aka rattaba hannu
kan wannan yarjejeniya a shekara ta 2015, tana nan yadda take, illa dai kawai
wasu kasashe ne ba su yin aiki da kamar yadda suka rattaba hannu, saboda haka
su dawo su yi aiki da ita ne mafita, ba rubuta wata sabuwar yarjejeniya ba.
Wannan bayani na gwamnatin Rasha na
zuwa a matsayin martani a kan bukatar da gwamnatocin Jamus, Burtaniya da kuma
Faransa suka gabatar ne, da ke neman a sake rubuta wata yarjejeniya kan shirin
Iran na nukiliya kamar yadda gwamnatin Amurka ta bukata, domin a saka wasu
batutuwa na daban da basu da alaka da shirin nukiliyar Iran a cikin yarjejeniyar.
015