​Masanin Tsaro: Amurka Da Isra’ila Ke Da Hannu Wajen Kisan Mohsen Fakhrizade

2020-12-07 09:32:08
​Masanin Tsaro: Amurka Da Isra’ila Ke Da Hannu Wajen Kisan Mohsen Fakhrizade

Wani masani kan harkokin siyasar kasa da kasa da tsaro daga kasar Iraki Juma’a Alatwani ya sheda cewa tabbas Amurka da Isra’ila ne suka kashe Fakhrizadeh da sauran masanan kasar Iran da aka yi wa kisan gilla a baya.

Ya ce irin wannan mataki yana nuni da yadda Amurka da Isra’ila suke kallon tasirin kasar ta Iran a dukkanin bangarori a yankin gabas ta tsakiya, kuma suna kallon kasar a matsayin babbar barazana da za ta iya zama babban karfe kafa ga manufofinsu na siyasar mulkin mallaka da mamaye arzikin al’ummomin kasashen yankin.

Ko shakka babu kisan Mohsen Fakhrizadeh ya zo ne a daidai lokacin da Amurka da Isra’ila da kuma ‘yan korensu a yankin da suke yi musu amshin shata daga cikin kasashen larabawa masu tsananin kiyayya da Iran, suke son daukar fansa a kan kasar, sakamakon gagarumin ci gaban da ta samu a cikin kankanin lokaci a bangarori daban-daban na ilimi, da hakan ya hada har da bangaren nukiliya.

Masanin na kasar Iraki ya ce, tabbas Iran za ta mayar da martani kan wannan babban laifi na ta’addanci, kuma martanin zai zama mai girgizawa ne matuka ga masu hannu a cikin lamarin. Ya ce kasantuwar kasar ta Iran tana da masaniya akan irin wadannan lamurra, ta san hanyoyin da zata bi domin mayar da martanin da ya dace.

Dangane da yadda majalisar dinkin duniya ta mayar da martani kan lamarin kuwa, ya bayyana cewa abin kunya ne, domin kuwa laifi na ta’addanci da aka aikata a cikin kasa mai ‘yanci kuma cikakkiyar mamba a wannan majalisa, amma sai majalisar ta takaita da yin Allawadai kawai, maimakon yin kira da a gudanar da dabincike domin gano masu laifin domin su fuskanci hukunci, kamar yadda take yi idan irin wannan ta faru a kan wasu kasashen.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!