Kotu Ta Dage Shari’ar Sheikh Zakzaky Zuwa Ranakun 25-26 Ga Watan Janairun Shekara Mai Kamawa

2020-11-19 21:41:42
Kotu Ta Dage Shari’ar Sheikh Zakzaky Zuwa Ranakun 25-26 Ga Watan Janairun Shekara Mai Kamawa

Kotun da ke sauraren shari’ar da ake wa jagoran harkar Musulunci a Nijeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky a jihar Kaduna ta dage ci gaba da sauraren karar har sai zuwa ranakun 25-26 ga watan Janairu na shekara mai kamawa don ba da dama wa masu kara su ci gaba da gabatar da shaidunsu.

A safiyar yau din nan ne dai aka sake dawowa babbar kotun jihar Kadunan don ci gaba da shari’ar da ake yi wa Sheikh Ibrahim Zakzaky din da mai dakinsa malama Zeenat Ibrahim bayan da alkalin kotun y adage shari’ar a jiya zuwa yau don ci gaba da sauraren shaidun da masu shigar da kara suke son gabatarwa don tabbatar da zargin da suke yi wa Shehin malamin da mai dakinsa.

A zaman na yau dai, masu shigar da karar sun gabatar da shaidansu na uku wanda shi ne Muhammad Abba Girei wanda darakta ne a helkwatar rundunar tsaro ta farin kaya ta Nijeriyan DSS wanda kuma shi ne aka dora masa alhakin kula da Shehin malamin da mai dakin nasa bayan da sojoji suka mika su hannun hukumar ta DSS.

Shaida na biyu kuma da masu shigar da karar suka gabatar da wasu shaidu guda uku na daban wadanda mazauna unguwar Gyallesu unguwar da malam Zakzaky din yake zaune kafin harin da aka kai masa da kuma kama shi, wanda suka yi bayani kan halin da suke ciki tun lokacin da Sheikh Zakzaky din ya dawo unguwar.

Toh bayan tambayoyi da amsa tsakanin lauyoyin Sheikh Zakzaky da matarsa da shaidun da masu shigar da karar suka gabatar, daga baya dai alkalin kotun ya bisa bukatar masu shigar da kara wadanda suka ce za su ci gaba da kawo wasu shaidun don haka suna bukatar karin lokaci, ya dage ci gaba da sauraren shari’ar har sai zuwa ranakun 25-26 ga watan Janairu mai kamawa.

Gwamnatin jihar Kaduna din dai tana zargin Sheikh Ibrahim Zakzaky din da mai dakinsa ne da laiffuffukan da suka hada da kisan kai, taro ba bisa ka’ida ba, tada hankali da dai sauransu lamarin da wadanda ake zargin suka musanta.

Sheikh Zakzaky da mai dakin nasa suna tsare ne dai tun daga watan Disamban 2015 har zuwa yau din nan duk kuwa da umurnin da wasu kotuna a Nijeriya suka bayar na a sake su.

014

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!