Boko Haram Ta Kashe Sojojin Chadi 92

2020-03-25 09:39:38

Rahotanni daga Chadi na nuni da cewa sojojin kasar akalla 100 ne suka rasa rayukansu a wani hari da ake kyautata zaton na kungiyar boko haram ne.

Harin an kai shi ne a yankin Boma dake tafkin Chadi inda kungiyar ta zazafa kai hare haren ta a ‘yan watannin baya bayan nan.

Wannan dai shi ne hari mafi muni da aka taba kai wa kan sojojin kasar ta Chadi.

Shugaban kasar Idriss Deby, wanda ya ziyarci inda aka kai harin, ya sha alwashin daukar mummunar fansa kan wadanda suka kai harin.

Wasu majiyoyin soji sun ce akwai yiyuwar adadin sojojin da suka mutu ya fi hakan, sannan mayakan sun yin garkuwa da wasu da kuma awan gaba da tarin makamai a harin na ranar Litini wanda aka kwashe kusan sa’o’I 7 ana fafatawa.Tags:
Comments(0)