Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da takwaransa na kasar Masar a birnin Alkahira
Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi wanda yanzu haka yake kasar Masar ya gana da takwaransa na kasar Badr Abdel Ati a birnin Alkahira na kasar Masar, inda a tattaunawar bangarorin biyu suka fi mayar da hankali kan batutuwan da suka fi muhimmanci a yankin Gabas ta Tsakiya musamman abubuwan da ke faruwa na yaki a Gaza da Lebanon.
Bangaren tattaunawan ya fi mayar da hankali ne kan sabbin abubuwan da suke faruwa a Gaza da Lebanon, inda ministocin harkokin kasashen biyu sun jaddada wajabcin dakatar da laifukan da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa kan Falasdinawa, Araqchi a rangadinsa ya zagaya kasashe da suka hada da Lebanon, Siriya, Saudiyya, Qatar, Iraq, Oman da Jordan, tare da ganawa da manyan jami’an kasashen.
Alkahira dai shi ne zango na takwas da ministan harkokin wajen Iran ya kai ziyarar aiki a yankin a wani bangare na yunkurin diflomasiyya na Iran na neman dakatar da yakin Gaza da Lebanon.