Search
Close this search box.

 Ziyad Nakhala: Iran Tana Taka Gagarumar Rawa Wajen Taimakawa  Falasdinawa ‘Ya Gwagwarmaya

 Babban magatakardar kungiyar Jiahdul-Islami ta Palasdinu wanda yake ziyarar aiki a nan Iran, ya bayyana cewa; A cikin watannin bayan nan Iran tana taka gagarumar

 Babban magatakardar kungiyar Jiahdul-Islami ta Palasdinu wanda yake ziyarar aiki a nan Iran, ya bayyana cewa; A cikin watannin bayan nan Iran tana taka gagarumar rawa a fagen taimawa ‘yan gwgawarmaya a Falasdinu

Nakhla ya gana da ministan harkokin wajen Iran Amir Abdullahiyan yana mai yin ishara da yadda shi kanshi ministan yake bin diddigin abubuwan da suke tafiya.

Bugu da kari babban sakataren kungiyar ta Jihadul-Islami ya jinjinawa gwamantin jamhuriyar musulunci ta Iran da al’ummarta akan goyon bayan da suke bai wa al’ummar Falasdinawa, sannan ya kara da cewa; Ba domin taimakon na Iran ba,to da al’ummar Falasdinu ba su iya jajurcewa ba.

Shi dai babban magatakardar kungiyar ta Jihadul-Islami  Ziyad Nakhala tare da shugaban kungiyar Hamas suna ziyarar aiki anan Iran, inda suke ganawa da manyan jami’an gwamnatin kasar da su ka hada da jagoran juyi Ayatullah Sayyid Ali Khamnei  da kuma shugaban kasa Ibrahin Ra’isi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments