Zanga-Zangar Nuna Goyon Baya Ga Al’ummar Falasdinu A Kasar Pakistan

Miliyoyin mutane ne a kasar Pakistan suka gudanar da zanga-zangar neman hukunta shugabannin mamayar Isra’ila kan laifukan da suka aikata Miliyoyin ‘yan kasar Pakistan ne

Miliyoyin mutane ne a kasar Pakistan suka gudanar da zanga-zangar neman hukunta shugabannin mamayar Isra’ila kan laifukan da suka aikata

Miliyoyin ‘yan kasar Pakistan ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Islamabad fadar mulkin kasar domin nuna goyon bayansu ga al’ummar Palasdinu da kuma gwagwarmayarsu. Mahalarta zanga-zangar sun bukaci kawo karshen zaluncin yahudawan sahayoniyya kan al’ummar Falasdinu tare da hukunta shugabannin mamayar Isra’ila kan laifukan da suka aikata kan al’ummar Falasdinu, tare da jaddada goyon bayansu ga bangarorin da suke goyon bayan Falasdinawa.

A karkashin taken “Zanga-Zangar Miliyoyi Domin Goyon Bayan Gaza”, ‘yan Pakistan sun taru a birnin Islamabad fadar mulkin kasar, domin nuna goyon bayansu ga al’ummar Falasdinu, a daidai lokacin da suke neman kawo karshen zaluncin yahudawan sahayoniyya da kuma aayyukan laifukansu na aiwatar da kisan gilla kan Falasdinawa.

Babban jami’i a kungiyar Islama ta Pakistan, Kashif Chaudhry, ya shaida wa tashar talabijin ta Al-Alam cewa: Wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya ya wuce dukkan iyakoki, kuma babu hujjar yin shirun kasa da kasa, inda shirun nasu ke fayyace makirci da makarkashiyarsu na goyon bayan ‘yan sahayoniyya a yunkurinsu na share Falasdinawa daga kan doron kasa, duk da cewa ‘yan gwagwarmaya suna ci gaba da kokarinsu wajen kare al’ummarsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments