Zanga-Zangar Al’ummar Moroko Kan Kin Amincewa Da Ba Takardan Izinin ‘Yan Kasa Ga Yahudawa

Al’ummar Moroko sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da shirin mahukuntan kasar na bai wa yahudawa bakin haure takardun zama ‘yan kasa A cikin

Al’ummar Moroko sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da shirin mahukuntan kasar na bai wa yahudawa bakin haure takardun zama ‘yan kasa

A cikin wani yanayi mai cike da cece-kuce, gwamnatin Moroko ta sanar da cewa ta samu wani daftarin kudurin doka da aka gabatar wa Majalisar Dokokin Kasar da ke neman bai wa ‘ya’ya da jikokin Yahudawa takardar zama cikakkun ‘yan kasa a Moroko.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wata kungiya mai zaman kanta ta kasar Moroko da take adawa da duk wani matakin kulla alakar jakadanci da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi gargadi kan hadarin da ke tattare da zartar da wannan kudiri, domin ta ce yana yin barazana ga zaman lafiyar Masarautar, saboda hakan na iya haifar da ba da izinin zama ‘yan kasa ga tsagerun yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida da sojojin yahudawa da suke da hannu a aiwatar da “Kisan kare dangi” kan al’ummar Falasdinu.

Ma’aikatar Moroko da ke kula da hulda da Majalisar Dokokin Moroko ta ce ta samu koke a fagen doka tana neman a ba da izinin zama ‘yan kasar Moroko ga dukkan yara da jikokin yahudawa da aka haifa a Moroko.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments