Shugaban kungiyar Harka Islamiya ta Najriya Sheikh Ibrahim Zakzaky ya bayyana cewa samuwar JMI sanadiyyar yunkurin Imam Hussain (a) ne, wanda ya sami nasara tare da jagorancin Imam Khomaini (q) a shekara 1979.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a taron juyayin Ashoora na shekara ta 1446 a Abuja. Ya kuma kara da cewa sauran kungiyoyi masu gwagwarmaya gaba daya, a Lebanon da Iraki da Yemen duk sun sha ne da ilmantarwan Imam Hussain (a).
A lokacinda yake hira da yan Jaridu shugaban IMN ya kara da cewa tsarin Democradiyya wanda kasashen yamma da Amurka suke tutiya da shi ba gaskiya bane saboda dubban daruruwa ko kuma miliyoyin mutanen wadannan kasashen su suna goyon bayan Falasdinawa. A yayinda gwamnatocinsu na taimakawa HKI.
Ya kara da cewa gwamnatocin kasashen yamma basa wakiltan mutanen kasashensu, kuma lokaci yayi da mutanen wadan nan kasashe zasu dauki al-amuran kasashensu a hannusu.