Zababben shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan wanda ya gana da ‘yan majalisar shawarar musulunci ta Iran, ya bayyana cewa; Abinda ya kawo mu shi ne lalubo hanyoyin da za a warware matsalolin al’umma.
Mas’ud Fizishkiyan ya kuma kara cewa; Na sha fada ina nanatawa a yayin muhawar yakin neman zabe da kuma a wannan majalisar cewa; Babu yadda za a iya tafiyar da kasa ta hanyar rikici da sabani, dole ne mu hada hannu wuri daya domin fuskantar matsalolin da suke a gabanmu; Abinda ya kamata mu yi kenan, mu warware matsalolin mutane.
Zababben shugaban kasar ta Iran ya kuma ce: Dukkanin kokarin d azan yi shi ne na biyawa mutane bukatunsu, mun zo ne domin warware matsalolin mutane.