Zababben shugaban kasar ta Amurka ya ce matukar mambobi kasashen wannan kungiyar ba su biya kudaden da ya kamata su bayar ba, tabbas Amurka za ta yi nazarin ficewa daga kungiyar ta Nato.
Zababben shugaban kasar ta Amurka wanda tashar talabijin din NBC ta yi hira da shi, ya bayyana cewa ya shata wa mambobin kungiyar wani layi da shi ne kasashe kamar Canada da sauran kasashen turai mambobi a kungiyar dole ne su kara yawan kudaden da suke bayarwa, ko kuma Amurkan ta yi tunanin barin Nato.
Tun bayan rushewar tarayyar Soviet, kungiyar ta Nato ta kara fadada da shigar da sabbin mambobi a cikinta.
Sai dai Amurkan ta raunana karfin kasashen na turai ta yadda ba za su iya yin wasu ayyuka masu alaka da tsaro ba, sai a cikin kungiyar ta Nato. Kuma har yanzu da kasashen na turai suke fuskantar hatsari daga Rasha, da kuma yiyuwar ficewar Amurka daga Nato, ba su yi wani yunkuri na tsayuwa da kafafunsu ta fuskar tsaro ba.
Daga lokacin barkewar yakin Ukiraniya, Amurka kadai ta ba ta taimakon kudaden da su ka kai dala biliyan 66, yayin da kasashen turai su ka bai wa wannan kasar da take yaki da Rasha, dala biliyan 65.
A lokacin da yake yakin neman zabe, Donald Trump ya yi alkawalin kawo karshen yakin Ukiraniya ta hanyar yin sulhu a tsakaninta da Rasha, sannan kuma da janye duk wani tallafi daga Amurka.