Zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Bin manyan manufofin siyasar kasa da shiryarwar jagoran juyin juya halin Musulunci sune mabudin warware sabanin da ke tsakaninsu.
A wata hira da ya yi da kafar yada labaran Jagoran juyin juya halin Musulunci, zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi nuni da matakai guda hudu da ya dauka na nada sabuwar majalisar ministocin gwamnatinsa, inda ya ce: Matakin farko shi ne sun sanar da kowa da kowa, jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyi da su gabatar da sunayen mutanen da za su iya taimakawa sabuwar gwamnatin kasar.
Ya kara da cewa: Abu na biyu, sun bukaci malaman jami’o’i da su gabatar da jerin alamomin da suka dace abi su wajen zaben wadannan mutane, kuma sun gabatar da wasu muhimman alamomi. Pezeshkian ya bayyana cewa; Mataki na uku shine tantance mutanen da aka gabatar bisa ga kwarewarsu da ba su darajar da suka cancanta.
Zababben shugaban kasar ya yi bayani game da mataki na hudu da cewa: Sannan bayan tantance su, a karshe za a gudanar da shawarwari da kokarin samun fahimtar juna da ta dace da jagoran juyin juya halin Musulunci don kai wa ga karshen abin da ake nema.
Har ila yau, zababben shugaban ya yi tsokaci kan gaba daya ma’auni da abubuwan da gwamnatin da ake son ta sa a gaba, inda ya ce: Kiyaye doka, kyakkyawar alaka, aminci, gaskiya, kyakkyawan suna, imani da manufofin jama’a, imani da dokoki da tsarin Jamhuriyar Musulunci, inda suke cikin mafi mahimmancin alamomi na gaba ɗaya don zaɓar waɗannan mutane.