Babban hafsan hafsoshin sojan Iran kuma mataimakin kwamandan soja, ya bayyana cewa; Nan gaba kadan sojojin za su karbi muhimman kayan aiki.
Rear Admiral Habibullah Sayyari wanda ya fadi hakan, ya kuma kara da cewa; Daga cikin muhimman kayan aiki da sojojin za su karba da akwai jiragen sama marasa matuki fiye da 1000.
Haka nan kuma ya ce; wadannan jiragen sama marasa matukin suna da kayan aiki na koli a jikinsu da za su kai hari kai tsaye.
Real Admiral Sayyari ya kuma kara da cewa, ba da jimawa ba, sojojin kasa na Iran za su karbi sabbin makamai da kayan aiki.