Gwamnatin Kasar Yemen ta sallami ma’aikatan katafaren jirgin ruwan kasuwancin mai suna ‘Galaxy Leader, da kuma jirgin nasu saboda goyon bayan tsagaita wuta a Gaza,
A ranar 19 ga watan Nuwamban shekarar ta 2023 ne sojojin kasar Yemen suka kama jirgin ruwan a kan tekin Maliya bayan ya sabawa dokar hana jiragen ruwan kasuwanci zuwa HKI wanda gwamnatin kasar ta Yemen ta kafa, saboda tallafawa al-ummar Falasdinu wadanda sojojin HKI suke masu kissan kare dangi a Gaza.
Labarin ya kara da cewa, gwamnatin kasar Yemen ta dauki wannan matakinne, don taimakawa tsagaita budewa juna wuta wuta da aka fara a ranar Lahadin da ta gabata a Gaza.
Ma’aikatan jirgin dai su 25 ne, wadanda suka fito daga kasashen daban-daban na duniya. Wadanda kuma suka hada da turawan ingila, Philipine da sauransu.
Ansarullah, ta ce, Sojojin Yemen sun kai hare-hare fiye da 100 kan jiragen ruwa daukar kaya da na yaki na kasashen Ingila da Amurka da kuma wasu kasashen wadanda suka sabawa dokarta, a tekun Red Sea, da mashigar ruwa na babaul mandam da kuma tekun arabia.