Yemen Ta Gargadi HKI Kan Ci Gaba Da Hana Shigar Kayakin Agaji Zuwa Yankin Gaza

Ana cikin zullumi kan sake barkewan yaki a Gaza, bayan da HKI ta ci gaba da hana shigowar kayakin zuwa cikin Gaza. Sannan kungiyar Ansarull

Ana cikin zullumi kan sake barkewan yaki a Gaza, bayan da HKI ta ci gaba da hana shigowar kayakin zuwa cikin Gaza. Sannan kungiyar Ansarull ta kasar Yemen ta yi barazanar daukar mataki a kan HKI idan ta ci gaba da hana shigar kayakin Agaji zuwa cikin gaza.

Abdullatif Al-washali wani dan siyasa a kasar ta Yemen ya bayyana cewa rufe mashigar Rafah ta inda kayakin agaji suke wucewa su shiga Gaza, wata hanya ce ta wahalarta mutanen yankin, kuma yana dai dai da cilla yaki a kan mutanen Gaza. Ya ce kasar Yemen tana iya daukar matakin soje kan HKI matukar wannan tocewar ta ci gaba.

Har’ila yau sojojiun kasar ta Yemen sun bayyana cewa inda HKI ta ci gaba da sabawa yarjeniyar da suka cimma da Falasdinawa a Gaza, sojojin suna iya daukar matakai wadanda zasu shafi cibiyoyin tsaro na HKI a cikin kasar Falasdinu da ta mamaye ko na wajen kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments