Shugaban Majalisar dokokin kasar Yemen Yahya Ali al-Ra’i ya aike da sako na gaggawa ga takwaransa na Masar Hisham Badwi akan labarun da suke Magana akan cewa; Majalisar kasar za ta yi zaman gaggawa bisa bukatar shugaba Abdul-Fattah al-Sisi domin tattauna bai wa sojojin kasar damar zuwa Saudiyya domin taya ta fada da Yemen.
Sakon na al-Ra’i ya kunshi nuna damuwa akan shigar sojojin Masar cikin yakin domin taya Saudiyya fada da Yemen, yana mai yin kira ga al-kahira da kar ta shiga cikin wannan yakin, maimakon haka ta mayar da hankali wajen lalubo hanyar siyasa ta warware matsalar.
Haka nan kuma ya yi Ishara da yadda Saudiyya ta shelanta yaki akan Yemen na tsawon shekaru 12,amma da aka yi yarjejeniyar tsagaita wuta sai ta ki aiki da dukkanin sharuddan da ta kunsa da za su kai ga samar da zaman lafiya.
Bugu da kari Saudiyya din ta tsananta takunkumai da killace kasar Yemen da ya kai ga bullar yunwa a wasu yankuna.
Al-ra’i ya zargi Saudiyya da karya tsagita wutar yaki ta hanyar kai wa filin saukar jiragen sama na San’a hari, haka nan akan muhimman cibiyoyin kasar na fararen hula.
Shugaban majalisar kasar ta Yemen ya kuma ce; abinda kasarsa take nema shi ne tsagaita wutar yaki da kawo karshen dukkanin killacewar da ta yi wa Yemen,don haka kamata ya yi Masar ta dauki matakin kawo karshen fada da rikici a cikin wannan yankin.
Ra’i ya ce, shigar Masar cikin wannan fada yana cin karo da tarihinta na hadewa da Yemen wanda ya kai ga kafa tarayya a tsakanin kasashen biyu.
A karshe ya yi Ishara da rawar Masar a cikin muhimman batutuwa da su ka shafi al’ummar larabawa da samo hanyoyi na siyasa domin warware matsalolin da suke fuskanta.