Yemen: Sojojin Yamen Sun Kai Hari Akan Jirgin Ruwan Amurka Mai Dakon Jiragen Yaki

A wata sanarwa da kakakin sojan Yemen Janar Yahya Sari ya yi a jiya da dare, ya bayyana cewa; sun kai hare-hare guda biyu akan

A wata sanarwa da kakakin sojan Yemen Janar Yahya Sari ya yi a jiya da dare, ya bayyana cewa; sun kai hare-hare guda biyu akan jiragen ruwan Amurka masu dakon jiragen yaki akan tekun “Red Sea’ da kuma tekun Larabawa.

Kakakin sojan na kasar Yemen ya kuma kara da cewa; Harin na farko sun kai shi ne akan jirgin ruwa mai dakon jiragen yaki na; “Abraham Lincol” a tekun Larabawa. Janar Sari ya ce sun yi amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango da kuma jiragen sama marasa matuki.

Har ila yau, kakakin sojan na kasar Yemen ya kuma ce sun kai wasu hare-haren akan wani jirgin ruwan na Amurka  da yake akan tekun; “Red Sea”.

Janar Sari ya ce sun kai wadannan hare-haren ne dai a matsayin martani na hare-haren da sojojin Amurka da Birtaniya suke kai wa kasar Yemen, sannan kuma a matsayin nuna goyon bayan Falasdinawa da taya su fada.

Bugu da kari janar Sari, ya dora wa Amurka da Birtaniya alhakin mayar tekun “Red Sea’ fagen yaki

A ranar Talata da safe ne dai kafafen watsa watsa labarun na Yemen su ka sanar da cewa, Amruka da Birtaniya su ka kai wa Hudaidah, Umran da Sa’adah hare-hare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments