Yemen: Saudiya Tana Karya Don Rufe Shan Kayenta A Yemen

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Yemen ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Saudia tana fakewa da karya don rufe shan kaye da take fuskanta a gaban sojojin

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Yemen ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Saudia tana fakewa da karya don rufe shan kaye da take fuskanta a gaban sojojin kasar Yemen a kudancin kasar, da kuma cikin kasar saudia.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na JMI ya nakalto, ma’aikatar na cewa, gwamnatin kasar Saudia ta sha bada sanarwan cewa sojojin yemen suna kaiwa wurare masu tsarki a kasar don jawo hankalin wawaye cikin larabawa da musulmi su ki mutanen Yemen ko ma su zo su taimaka mata.

Labarin ya kara da cewa gwamnatin kasar ta Saudia a daren Asabar ta sake bada sanarwan kakkabo makaman Yemen a kan birnin Makka mai tsarki don jawo hankalin musulmi larabawa ko daga wasu kasashen.

Bayanin ya kammala da cewa ton lokacinda saudia ta fara wannan karyar gwamnatin Yemen ta sha nanata cewa ba zata kai hare a kan garuruwa masu tsarki ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted