Tashar talabijin din ‘almasirha’ ta kasar Yemen ta bayar da labarin dake nuni da cewa; Daliban kasar sun yi Zanga-zangar da su ka bai wa taken: “Zuriyar da Za a yi fadan karshe da ita.”
Mahalarta Zanga-zangar ta yau sun fitar da bayanin bayan taro da a ciki su ka yi ishara da yadda duniya ta yi shiru wajen hana ‘yan sahayoniya kisan kiyashi a Falasdinu,tare da yin tir da hakan da kuma dora wa Amurka alhakin cigaba da yakin na Gaza.
Har ila yau, daliban na kasar Yemen sun yi jinjina ga takwarorinsu na jami’o’in Amurka da turai suke nuna goyon bayan Falasdinawa.
Daliban na kasar Yemen sun kuma yi kira da a kauracewa sayen duk wata haja kirar ‘yan sahayoniya da masu goyon bayansu.
A gefe daya kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas ta fitar da bayani da a ciki take jinjinawa jaruntar “Ansarullah” na kasar Yemen na hana jiragen ruwa zuwa tashishin jiragen ruwan HKI.