Yan wasan kasar Iran sun kammala gasar wasannin sada zumunci na kasashen musulmi wanda aka kammala a birnin Riyad na kasar Saudiya tare da lambobin yabo har 81.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan ya nuna cewa kasar Iran na daga cikin kasashen musulmi wadanda suke da kwarewa a wasannin motsa jiki daban daban.
Labarin ya kara da cewa an gudanar da wasannin ne daga ranar 6 ga watan Nuwamba zuwa 21 ga watan. Tare da fara wasu wasannin daga ranar 3 ga watan. Kasar Saudiya wacce ta dauki bakwancin wadan nan wasannin motsa jiki ta sami nasarar tattara yan wasannin motsa jiki na kasashen musulmi a duniya a cikin kwanaki kima 20 da suka gudanar da wasannin motsa jiki a tsakaninsu.
Kasar Iran wacce ta ji da yan wasa 190 ta shiga wasannin har guda 20 sannan ta fito da lambobin yabo na Zinari har guda 29, azurfa 19 da kuma tagulla 33, wanda kuma ya bata matsayi na 3 a karshen gasar ko wasannin motsa jiki. Tawagar yan wasan kasar Turkiyya ce ta zo na farko sannan Uzbekistan ta zo na biyu.