‘Yan Tawayen Sudan Sun Kai Hari Kan Gidan Yarin Al-Obeid Tare Da Kashe Fararen Hula Masu Yawa

Wani hari kan gidan yarin Al-Obeid yayi sanadiyyar mutuwa da jikkatan mutane da dama a kasar Sudan Ministan al’adu da yada labarai, kuma kakakin gwamnatin

Wani hari kan gidan yarin Al-Obeid yayi sanadiyyar mutuwa da jikkatan mutane da dama a kasar Sudan

Ministan al’adu da yada labarai, kuma kakakin gwamnatin Sudan, Khaled Al-Aiser, ya tabbatar da cewa: Mutane 20 ne suka mutu, yayin da wasu 50 na daban suka jikkata a wani harin da ‘yan ta’addar Daglo na  kungiyar Rapid Support Forces masu aikata laifuka suka kai hari kan gidan yarin Al-Obeid.

Al-Aiser ya bayyana cewa: Harin da aka kai ya hada da asibitin birnin, inda ya yi sanadin mutuwar mutane musamman majinyata masu yawa tare da raunata wasu kimanin 50, wadanda dukkansu fararen hula ne, yana mai cewa wannan yana daga cikin manyan laifukan yaki.

Ministan ya kara da cewa: “Abin da ya faru a gidan yarin Al Obeid, babban laifin yaki ne, wanda ya kara tabbatar da cewa: Dakarun Kkai daukin gaggawa na Rapid Support Forces da magoya bayansu ‘yan ta’adda ne da suke cin zarafin fararen hula a Sudan.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments