Gwamnatin Sudan ta zargi ‘yan tawayen kasar na dakarun kai daukin gaggawa da kai hari kan ayarin motocin agaji kai a yankin Darfur
Gwamnatin Sudan ta sanar da cewa: “Dakarun kai daukin gaggawa sun kai hari kan ayarin motocin agajin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Darfur ta Arewa ta hanyar jiragen sama marasa matuka ciki.”
A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Sudan ta bayyana matukar bacin ranta tare da tofin Allah tsine da Allah wadai kan wannan mummunan lamari, tana mai jaddada cewa: “Yunkuri ne na ganganci na nufin toshe kungiyoyin agaji da dakile ayyukansu na kai kayan agaji ga fararen hula da suka makale a birnin El Fasher da sansanonin gudun hijira.”
Sanarwar ta ce “Hare-haren masu laifi sun yi sanadin lalata wasu manyan motocin Majalisar Dinkin Duniya, da kashe wasu masu gadi, da direbobi, da fararen hula, da kuma jikkata wasu jami’an tsaro da ke tare da ayarin motocin.”
Gwamnatin Sudan ta tabbatar da cewa: Harin ya saba wa dokokin jin kai na kasa da kasa, kuma kai tsaye da gangan ne aka niyyar illa ga kokarin da gwamnati take yi, tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kasa da kasa, na kai agajin gaggawa ga fararen hula da ke cikin bukata a halin yakin basasar kasar.