‘Yan Takara Bakwai Na Fafatawa A Zaben Shugaban Kasa A Mauritania

A Mauritami ‘yan takara bakwai ne suka fafata a zaben shugaban kasar da aka kada kuri’arsa yau Asabar. Daga cikin ‘yan takaran har da Shugaba

A Mauritami ‘yan takara bakwai ne suka fafata a zaben shugaban kasar da aka kada kuri’arsa yau Asabar.

Daga cikin ‘yan takaran har da Shugaba Mohamed Ould Ghazouani mai barin gado.

Sauran jiga-jigan ‘yan takaran sun hada da mai rajin kare hakkin bil adama Biram Dah Abeid, wanda ya zo matsayi na biyu a zabukan shugaban kasa biyu da suka gabata, sai kuma shugaban jam’iyyar Tewassoul mai kishin Islama, Hamadi Ould Sidi El Mokhtar, mai karfin fada a ji a bangaren adawa a majalisar dokokin kasar.

Sama da ‘yan Mauritaniya miliyan 1.9 ne aka kira zuwa rumfunan zabe domin zaben shugaban kasa.

A wani mataki na tabbatar da gudanar da zaben cikin lumana, gwamnati ta kafa wata hukuma ta kasa da ke da alhakin sa ido kan zaben, inda aka baza masu sa ido 600 a duk fadin kasar, duk da cewa ‘yan adawa na nuna shakku game da su.

Kungiyar Tarayyar Afirka ta aika da masu sa ido 27 na gajeren lokaci.

Idan babu wani dan takara da ya iya samun akalla kashi 50% na kuri’un, za a shirya zagaye na biyu a ranar 14 ga watan Yuli.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments