‘Yan Ta’adda Sun Kashe ‘Yan Sandan Iran 5 A Wani Harin Ta’addanci A Garin Iranshahr Na Iran

‘Yan sandan Iran 5 ne suka yi shahada a wani harin ta’addanci da aka kai musu a garin Iranshahr da ke lardin Sistan da Baluchestan

‘Yan sandan Iran 5 ne suka yi shahada a wani harin ta’addanci da aka kai musu a garin Iranshahr da ke lardin Sistan da Baluchestan na Iran

A yau Juma’a wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari kan wata motar ‘yan sanda a yankin Daman da ke Iranshahr a lardin Sistan da Baluchestan na kasar Iran. Harin ta’addancin ya yi sanadiyar shahada da jikkata wasu jami’ai.

Cibiyar yada labarai ta ‘yan sanda ta Sistan da Baluchestan ta sanar da faruwar lamarin, inda ta ce: A ‘yan sa’o’in da suka gabata ne wasu ‘yan ta’adda suka kai hari kan wasu jami’an ‘yan sanda biyu da ke sintiri a shingen binciken ababan hawa na Daman Iranshahr, wadanda ke cike da samar da tsaro ga ‘yan kasar a kan hanyar Khash-Iranshahr.

A cewar wannan rahoto, abin takaici, jami’an tsaro biyar da jami’an ‘yan sanda masu sintiri sun yi shahada a wannan ta’addancin.

Ana ci gaba da gudanar da aikin bincike domin ganowa da kuma bin diddigin ‘yan ta’adda, kuma za a bayyana sakamakon nan gaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments