Search
Close this search box.

‘Yan Majalisar Dattijan Amurka Sun Gargadi Kotun ICC Kan Daukar Mataki A Kan Isra’ila

Wasu gungun ‘yan majalisar dattijan Amurka sun gargadi babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) kan yuwuwar daukar duk

Wasu gungun ‘yan majalisar dattijan Amurka sun gargadi babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) kan yuwuwar daukar duk wani mataki da kotun ka iya yi, na bayar da sammacin kame jami’an gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila kan yakin kisan kare dangi da suke  ci gaba da yi a zirin Gaza.

An mika gargadin ne a cikin wata wasika mai zafi da Sanatocin suka aike wa lauya dan kasar Birtaniya kuma babban mai shigar da kara na kotun (ICC).

Sanatocin da suka hada da Tom Cotton, Mitch McConnell, Rick Scott, Tim Scott, Ted Cruz, da Marco Rubio, su ne suka rubuta a cikin wasikar ga kotun duniya cewa, “Idan kuka taba Isra’ila, to Mu ma za mu taba ku.”

Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC da ke birnin Hague a halin yanzu tana gudanar da bincike kan laifukan yaki da sojojin Isra’ila suka aikata a Gaza.

Tuni dai aka yi ta rade-radin cewa kotun na iya bayar da sammacin kama wasu manyan jami’an Isra’ila kan yakin da ake yi a Gaza tun daga watan Oktoba da ya gabata, wanda ya yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa kusan 35,000 galibinsu mata da kananan yara.

Jami’an Isra’ila da ke fuskantar wannan sammaci dai sun hada da Firayim Minista Benjamin Netanyahu, ministan yaki soji Yoav Gallant, da babban hafsan hafsan sojin Isra’ila Herzi Halevi.

Sanatocin na Amurka, sun ce ta hanyar yin aiki da wannan sammacin a kan jami’an gwamnatin Isra’ila, kotun hukuntan manyan laifuka ta MajalisarDinkin Duniya ICC, za ta kasada, wadda za ta kai ta ga rasa samun goyon bayan Amurka.

Baya ga hakan kuma, sanatocin na Amurka, sun gargadi mai shigar da kara na kutun duniya cewa, idan kotun ta fitar da sammaci kan jami’an Isra’ila, to Amurka za ta kakaba takunkumai a kan alkalai da masu shigar da kara na kotun da iyalansu.

A cikin watan Janairu, Kotun Duniya (ICJ), bangaren shari’a na Majalisar Dinkin Duniya a kan manyan laifuka, ta yanke hukuncin cewa “akwai hadarin gaske na kisan kare dangi a Gaza da kuma ci gaba da cutar da fararen hula, tun daga lokacin Kotun ta umarci Tel Aviv da ta dauki dukkan matakan hana kisan kiyashi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments