Daruruwan manya-manyan yan kasuwa daga kasar Rasha ne zasu ziyarci kasuwar baje koli na kayakin da ake kerawa a kasar Iran wadanda kuma za’a kaisu kasar Rasha.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa ana saran yan kasuwa daga kasar Rasha 100-150 ne, zasu ziyarci kasuwar baje koli wanda za’a gudanar a birnin Tabriz na arewa maso yammacin kasar Iran daga ranar 12-15 ga watan Fabrayru na shekara ta 2025 mai zuwa.
Labarin ya kara da cewa duk kayakin da za’a baje kolinsu a kasuwar, wadanda aka shirin kaisu kasuwannin kasar Rasha ne.
Habib Mahouti shugaban kasuwar baje koli ta kasa da kasa ta birnin Tabriz ya fadawa kamfanin dillancin labaran IP kan cewa, kan cewa, wannan itace kasuwar baje koli ta farko wanda aka kebe don kasar Rasha..
Banda haka ya ce: Kayakin da za’a baje kolinsu sun hada da kayakin da suke da dangantaka da man fetur, kayakin hannu wadanda suka hada da dardumu, da kayakin abinci na masana’antu, da kuma na kamfanoni.
Daga karshen shugaban kasuwar baje kolin yace, kasuwar zata zama wata dama ce ga kasashen biyu wajen bunkasa harkokin kasuwanci a tsakaninsu.