Gaza: Adadin ‘Yan Jarida Da Suka Yi Shahada Ya Kai 232

‘Yan jarida akalla 232 suka yi shahada sannan wasu 122 sun rasa rayukansu saboda masifar yunwa a yankin Zirin Gaza! Yakin kisan kare dangi da

‘Yan jarida akalla 232 suka yi shahada sannan wasu 122 sun rasa rayukansu saboda masifar yunwa a yankin Zirin Gaza!

Yakin kisan kare dangi da ake yi a zirin Gaza yana ci gaba da lakume rayukan Falasdinawa da dama a kowace rana, manya da kanana…ta hanyar jefa bama-bamai, kisa, killace yankin da kakaba masifar yunwa.

A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, an kashe Falasdinawa da dama tare da jikkata wasu daruruwa, ciki har da masu neman agaji, sakamakon hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wata makaranta da ke dauke da ‘yan gudun hijira a unguwar al-Rimal da gidaje da sansanonin ‘yan gudun hijira a yankunan al-Amal, al-Tuffah, da al-Nasr, dake gabashi, arewacin Gaza.

Hakazalika an sha kai hare-hare ta sama a yankunan al-Balad da al-Amal da ke Khan Yunus da ke kudancin zirin Gaza, da kuma harin bama-bamai da jiragen yakin sojin mamayar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted