‘Yan Gwagwarmayar Falasdinawa Sun Raunata Wani Babban Jami’in Sojan Gwamnatin Isra’ila

‘Yan gwagwarmaya sun jikkata wani babban jami’in sojan gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin arewacin Gaza Rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila ta ce: Wani babban

‘Yan gwagwarmaya sun jikkata wani babban jami’in sojan gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin arewacin Gaza

Rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila ta ce: Wani babban jami’in sojanta ya sami  mummunan rauni a ranar Laraba bayan da ‘yan bindiga suka bude wuta kan rundunar sojin mamayar Isra’ila kusa da Green Line a arewacin Gaza. Kafafen yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun tabbatar da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila za ta mayar da martani mai tsanani kan haka.

Wata sanarwar rundunar sojin mamayar Isra’ila ta kara da cewa ta kai hare-haren atilare da jiragen sama kan yankunan da suke yankin Gaza a matsayin mayar da martani ga harin da aka kai wa sojojinta a arewacin yankin. Ta dauki harin a matsayin karya yarjejeniyar tsagaita wuta.

Jaridar Yediot Aharonot ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta ambato rundunar sojin Kudu ta sojojin mamayar Isra’ila tana cewa: Tana shirin kai hari kan wuraren soji a Gaza a matsayin martani ga raunin da jami’in ya samu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments