‘Yan Gwagwarmayar Falasdinawa Sun Kai Hare-Hare 13 A Cikin Sa’o’i 24 Kan ‘Yan Sahayoniyya

‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa sun kaddamar da hare-haren mayar da martani kan sojojin mamayar Isra’ila guda 13 a Gabar yammacin Kogin Jordan a cikin sa’o’i 24

‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa sun kaddamar da hare-haren mayar da martani kan sojojin mamayar Isra’ila guda 13 a Gabar yammacin Kogin Jordan a cikin sa’o’i 24 da suka gabata

‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa sun ci gaba da kai hare-haren daukan fansa a Gabar yammacin kogin Jordan a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, a matsayin wani bangare na yakin “Ambaliyar Al-Aqsa”, kuma sun kai hare-hare 13 kan sojojin mamayar Isra’ila da kan matsugunan tsagerun yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida.

Cibiyar yada labarai ta Falasdinu ta “Ma’ati” ta nuna faifan bindiyo na yadda ‘yan gwagwarmayar suke kai hare-haren daukan fansa a yammacin jiya Asabar da makamai masu linzami da tayar da bama-bamai gami da tarwatsa motocin yakin sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila baya ga musayar wuta da sojojin mamayar Isra’ila.

Cibiyar ta yi nuni da cewa: Matakan da ‘yan gwagwarmayar suka dauka sun hada da arangama da makamai da jifa da duwatsu a wurare daban daban guda 9 a gabar yammacin kogin Jordan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments