‘Yan Gwagwarmaya  Sun Kashe Sojojin Mamaya Biyu A Wani Kwanton Bauna A Arewacin Gaza

Sojojin HKI sun amabci cewa sojoji biyu sun halaka a wani kwanton bauna da mayaka a Gaza su ka yi, daga ciki har da kwamandan

Sojojin HKI sun amabci cewa sojoji biyu sun halaka a wani kwanton bauna da mayaka a Gaza su ka yi, daga ciki har da kwamandan rundunar “Folcan”.

Kakakin sojan HKI ya bayyana cewa wanda aka kashe din shi ne Manjo Shahir Natna’il, sai kuma Midgal Haimik a wani fada da aka yi a arewacin Gaza.

 Wasu kafafen watsa labarun HKI sun ambata cewa mayakan kungiyar gwagwarmaya ta Hamas sun yi wa sojoji kwanton bauna a wasu wurare biyu mabanbanta.

 A bisa kididdigar sojojin HKI adadin wadanda aka kashe zuwa yanzu a yakin Gaza, sun kai 911.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted