Bayan gushewar kwanaki 300 daga “Guguwar Aqsa” ‘yan gwgawarmaya daga Gaza, sun kai hari mafi tsanani akan matsugunan ‘yan hsare wuri zauna wanda yake a kusa da Gaza ta hanyar harba makamai masu linzami da yawa.
Wannan harin da makamai masu linzami ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan gwagwarmayar su ka kai wasu hare-haren akan sojojin mamayar HKI da su ka yi kutse a cikin wani yanki na Gaza.
Kakakin dakarun “Kassam” ya sanar da cewa; Sun kai harin ne da makamai masu linzami a zango biyu, inda a kowane lokaci su ka harba 10 a cikin sa’a daya daga marecen jiya juma’a.
A wani hari na hadin gwiwa da dakarun “Kata’ibu shuhada’u Aqsa, da Kaba’ibul-Ansar, sun harba makamai masu linzami da dama akan sansanin sojojin HKI na “Fajjah’.
Ita ma rundunar Shahid Umar al-Qasim ta sanar da kai wasu jerin hare-haren akan yankin “Karam Abu Salim” ta hanyar harba makamai masu linzami samfurin 107 mai cin gajeren zango.