Labaran da suke fitowa daga Jihar Zamfara na arewa maso yammacin Tarayyar Najeriya, sun bayyana cewa wasu yan bindiga sun yi garkuwa ko sun sace mutane 43 a unguwar Kakidawa na gidan-gona a karamar hukumar Maradun na jihar.
Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto wasu mutanen da basa son a bayyana sunayensu suna cewa, al-amarin ya auku ne a daren Lahadi, da misalign karfe biyu na dare.
Sun kuma kara da cewa hare-haren sun sa, mutane da dama suka shiga daji, amma yan bindigan sun kama mutane 43. 3 daga cikinsu manyan mutane ne, a yayinda saura 40 kuma, sun kasance mata da yara.
Labarin ya kara da cewa yan bindigan sun farwa garin ne a dai-dai lokacinda suke harbi na ‘kan mai uwa da wabi’ kafin ku shiga gida-gida su kama mutane 43.
Majiyar mutanen garin ta bayyana cewa ya zuwa yanzu dai, yan bindigan basu kira wani ba don jin abinda suke bukata na sako mutanen.