Search
Close this search box.

Yahudawan Sahayoniyya Suna Zanga-Zangar Neman Kulla Yarjejeniyar Sakin Fursunoni

Zanga-zangar neman kulla yarjejeniyar musanyar fursunoni a haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da yin kamari a tsakanin yahudawan sahayoniyya Rahotonni sun bayyana cewa: Titunan

Zanga-zangar neman kulla yarjejeniyar musanyar fursunoni a haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da yin kamari a tsakanin yahudawan sahayoniyya

Rahotonni sun bayyana cewa: Titunan yankunan da aka mamaye sun cika makil da masu zanga-zangar yin kira da a gaggauta kulla yarjejeniyar musayar fursunoni da kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa, suna masu neman shugabannin yahudawan sahayoniyya su hana fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu shirinsa na dakile yunkurin da ake yi na kammala yarjejeniyar.

Yahudawan Sahayoniyya sun fito a birnin Tel Aviv da sauran garuruwan haramtacciyar kasar Isra’ila suna kira da a gaggauta aiwatar da yarjejeniyar musayar fursunoni don dawowar ‘yan uwansu da suke hannun ‘yan gwagwarmaya.

Har ila yau, masu zanga-zangar sun rufe wani babban titi a yankin Galilee na sama domin nuna adawa da yanayin yankunan da suke arewacin haramtacciyar kasar Isra’ila.

Jaridar Yedioth Ahronoth ta haramtacciyar kasar Isra’ila a rahoton da ta nakalto daga majiyoyi masu tushe cewa: Nan da kwanaki masu zuwa za su kasance sun tabbatar da yiwuwar cimma yarjejeniyar musayar fursunoni da bangarorin gwagwarmayar Falasdinawa a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments